Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rushewar wani gini ya rutsa da wasu mutane a Nijeriya
2020-07-25 16:04:03        cri
Wani gini mai hawa biyu da ya rushe a yankin Ebute Metta na jihar Lagos, cibiyar harkokin kasuwanci ta Nijeriya, ya rutsa da wasu mazauna, tare da jikkata wasu.

Wani mazaunin wurin mai suna Hakeem Baba, ya shaidawa Xinhua cewa, ma'aikatan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar na aikin ceto.

Ana ta kara damuwa game da karuwar rushewar gine-gine a cibiyar ta harkokin kasuwanci ta kasar.

Wani lokaci, a kan alakanta rushewar gine-ginen da rashin ingancin kayayyakin gini da kuma rashin sanya kwararru cikin harkokin gine-ginen. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China