Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta lashi takobin yaki da cin hanci tare da kwato kudaden da aka sace
2020-07-14 11:07:25        cri
Gwamnatin Nijeriya ta lashi takobin ci gaba da yaki da karuwar cin hanci, tana mai cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato dukkan dukiyar da aka sace.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda a ranar 7 ga wata, gwamnatinsa ta dakatar da Ibrahim Magu, mai rikon mukamin shugaban hukumar EFCC, mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa, ya ce babu wanda za a kyale a yaki da cin hanci.

Ministan shari'a na kasar Abubakar Malami, ya bayyana a ranar Juma'a cewa, shugaba Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu daga mukaminsa nan take, lamarin da zai ba kwamitin shugaban damar gudanar da bincike kansa, bisa doron doka.

EFCC da aka kafa a shekarar 2003, hukuma ce mai karfin doka dake binciken laifuffukan da suka shafi kudi, kamar halasta kudin haram da karbar na goro.

Hukumar ta yaki matsalolin cin hanci da rashawa ta hanyar gurfanar da wasu manyan mutane a gaban kotu, kama daga tsohon babban mai aiwatar da doka zuwa shugabannin bankuna da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China