Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Nijeriya ya kamu da COVID-19
2020-07-20 09:21:28        cri
Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya tabbatar da cewa, ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Geoffrey Onyeama ya wallafa jiya a shafinsa na Twitter cewa, biyo bayan sakamakon gwajin da aka masa, yana kan hanyarsa ta zuwa asibiti domin killace kansa tare da jinya.

Ya ce ya yi gwajin cutar COVID-19 a karo na 4, bayan ya ji alamun ciwon makoshi, kuma a wannan karon, sakamakon ya nuna ya kamu da cutar. Yana mai cewa, haka rayuwa ta gada, wata rana a yi nasara, wata rana kuma a yi rashinta.

Ministan na daya daga cikin jami'an gwamnati dake cikin kwamitin hadin gwiwa da shugaban kasar ya dorawa aikin dakile yaduwar cutar a kasar.

Kawo yanzu, an tabbatar da mutane 36,107 sun kamu da cutar COVID-19 a Nijeriya. Daga cikinsu, 14,938 sun warke, yayin da cutar ta yi ajalin 778. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China