Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun kashe mutane 24 a arewacin Nijeriya
2020-07-14 09:46:19        cri
Mutane akalla 24 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan wasu hare-hare 3 da 'yan bindiga suka kai kauyuka 3 dake yankin karamar Zango Kataf, na jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya, a karshen mako.

Shugaban karamar hukumar Zango Kataf, Elias Manza, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce tsagerun, wadanda ake zargin Fulani makiyaya ne, sun fara kai hari ne kauyen Chibob a ranar Juma'a da daddare, inda suka kashe mutane 9 tare da ji wa wasu da dama munanan raunuka da kuma kona gidaje da dama.

Ya kara da cewa, sun kuma kai makamancin harin kauyen Sabon Kaura, inda suka kashe mutane 15 a daren, yayin da aka kai hari na 3 kauyen Ungwan Audu, a ranar Lahadi da daddare, inda a nan ma aka kone gidaje da gonaki da dama tare da jikkata mutane da yawa.

Kawo yanzu, rundunar 'yan sandan jihar bata tabbatar da aukuwar harin ba.

Tun farkon shekarar nan ake ta samun rahoton jerin hare-haren 'yan bindiga a arewacin Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China