Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin a Najeriya ya mika gudunmawar kayayyakin yaki da cutar COVID-19 ga Najeriya wanda farfesa Peng Liyuan ta bayar a madadin gwamnatin kasar Sin
2020-07-16 10:45:14        cri

A ranar 15 ga watan Yulin shekarar 2020, ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriya da gidauniyar A'isha Buhari, uwargidan shugaban kasar Najeriya, sun halarci bikin mika gudunmawar da farfesa Peng Liyuan ta bayar na kayayyakin yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a madadin gwamnatin kasar Sin.

A cikin jawabinsa, jami'in diflomasiyyar kasar Sin, Zhao Yong, ya ce a madadin gwamnatin Sin, farfesa Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ta bayar da gudunmawar kayayyakin yaki da cutar COVID-19 ga Najeriya domin taimakawa mutanen Najeriya, musamman mata, kananan yara, matasa da sauran marasa galihu, domin yakar cutar COVID-19. Kasar Sin a shirye take tayi aiki da Najeriya da nufin ingiza matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wakiliyar mai dakin shugaban Najeriya, babbar mai taimakawa shugaban kasa kan al'amuran mata Dokta Hajo Sani ta ce, A'isha Buhari tana matukar mutunta kyakkyawar alakar dake tsakaninta da farfesa Peng Liyuan. Gidauniyar uwargidan shugaban kasar Najeriyar zata yi kyakkyawan amfani da kayayyakin yaki da annobar domin karfafa matsayin lafiyar mata da kananan yara wajen yaki da annobar. An yi amanna cewa, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, Najeriya da Sin za su cimma nasarar kawo karshen annobar cikin kankanin lokaci.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China