Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kauyen Bohou na kokarin raya sana'ar yawon shakatawa irin ta yankin karkara
2020-06-29 14:46:52        cri

 

Tan Zhongxian, mazaunin kauyen Bohou dake birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin ne. Ya kuma dade da barin garinsu da iyalinsa, don cin rani a wasu wurare. Ko da yake kudin da ya samu ya karu, amma hakan bai faranta masa rai ba, burinsa shi ne kauyensu ma ya samu ci gaba.

A shekarar 2013, gwamnati ta tsaida kudurin yin gyare-gyare ga kauyen Bohou, kuma aka mai da sana'ar karbar baki a gidaje a matsayin wani muhimmin aiki. A karkashin taimakon kungiyar kula da aikin farfado da kauyuka, Tan Zhongxian ya yi amfani da wannan dama, ya koma garinsu don kafa karamin hotel a gidansa mai suna "Hai Na Jie".

 

 

Yanzu mazauna kauyen dake raya irin wannan sana'a suna ta karuwa, kuma burin Tan Zhongxian na wadatar da kauyensu ya cika.

Kamar sauran mazauna kauyen, Tan Zhongxian shi ma na cike da imani kan makomarsu a nan gaba. Ya bayyana cewa, yanzu a shirye yake, ya kara yin gyare-gyare ga hotel din da ya kafa a gidansa, da nufin kara raya sana'ar yawon shakatawa irin ta yankin karkara. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China