Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasan kwallo kan kankara ya taimaka wajen tabbatar da zaman rayuwar jama'a mai wadata
2020-07-04 16:27:14        cri

Zhou Yudi mai shekaru 40 a duniya, ya shafe shekaru 32 yana wasan kwallo kan kankara. A shekarar 2012, ya yi murabus daga gurbin aiki tasa mai samar da dimbin kudin shiga, ya koma garinsu, wato birnin Qiqihar don zama koci.

A waccan lokaci kuma, wannan wasa ba shi da masu sha'awa da yawa. Fili daya kawai ake da shi a birnin, kuma yawan 'yan wasa a birnin bai wuce 30 ba.

A shekarar 2017, an zartas da wata doka a majalisar wakilan jama'ar birnin, inda aka tsai da kudurin mai da mako daya kacal dake bayan Asabar ta farko ta watan Jarairun kowacce shekara, matsayin makon bikin wasan kwallo a kan kankara, da kuma mai da watan Yulin kowace shekara a matsayin lokacin wasan, inda har aka fadada filayen wasan, da nufin bunkasa shi.

Mazauna garin fiye da miliyan 1 sun himmantu wajen shiga wannan wasa, lamarin da ya sa wasan ya samun dimbin masa nuna sha'awa.

Zhou Yudi ya ce, ya yi farin ciki matuka da wannan wasa ya zama wani karfi mai inganci wajen kyautata zaman rayuwarsa. Mambobinsa sun karu sosai, kuma kudin shigarsa ya karu matuka, matakin da ya kara masa kwarin gwiwar gudanar da wannan aiki.

Ban da wannan kuma, saboda bunkasar wannan wasa a Qiqihar, fannonin dake da nasaba da shi su ma sun samu ci gaba sosai, alal misali, aikin gina dakunan wasa, ba da horo da samar da na'urorin wasa da kuma zirga-zirga da ma gidajen kwana da na abinci har ma da yawon shakatawa da sauransu, duk sun samu ci gaba baki daya, kamar yadda Zhou Yudi ya yi, karin mutane suna kokarin kyautata zaman rayuwarsu don samun wadata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China