Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana yi wa dukkan alummar birnin Urumqi binciken cutar COVID-19 a kyauta
2020-07-21 12:32:52        cri

Ofishin ba da jagoranci kan ayyukan dakile annobar COVID-19 na birnin Urumqi na jihar Xinjiang, ya ba da labarin cewa, domin hana yaduwar annobar COVID-19, bisa manufar yin bincike kan wadanda ya kamata a yi musu gwaji, da wadanda suke so a yi musu gwajin", an soma gudanar da aikin yin gwajin cutar a daukacin fadin birnin, inda yanzu haka ake gudanar da aikin bisa tsari kuma cikin sauri.

Ana gudanar da aikin gwajin ne kyauta, kuma ana maraba da mazauna birnin da su sa ido, da bayyana ra'ayin su game da gudanarwar aikin. Ga duk inda aka samu tabbaci na an karbi kudi domin aikin, ba kawai za a mayar da kudi ba ne, har ma za a yanke hukunci kan hakan bisa doka. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China