Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahotannin kafofin watsa labaran ketare game da tsare miliyoyin 'yan Uygur a jihar Xinjiang ta Sin ba su da tushe
2020-07-18 20:24:09        cri

A kwanakin baya bayan nan, wasu kafofin watsa labarai na kasashen ketare sun gabatar da wasu rahotanni, inda suka bayyana cewa, an tsare miliyoyin 'yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin, kuma an yi musu hukunci ba bisa ka'ida ba. A jiya Juma'a, wakilinmu ya samu labari daga jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur cewa, rahotannin ba su da tushe ko kadan.

Har kullum hukumomin kasar Sin na gurfanar da masu aikata laifuffuka bisa doka, misali idan aka kama 'yan ta'adda ko 'yan aware ko kuma masu tsattsauran ra'ayin addini, za a gudanar da bincike kan laifuffukan da suka aikata, kafin daga baya a yanke musu hukunci, idan kuma ba su aikata laifi mai tsanani ba, to za a kai su cibiyar ba da horo kadai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China