![]() |
|
2020-06-20 16:46:44 cri |
A cewar ofishin yada labarai na gwamnatin jihar, daga shekarar 2017 zuwa 2019, an samar da jimilar ayyukan yi 135,000 ga yankunan Kashgar da Hotan dake cikin matsanancin talauci.
An samar da horo kan fasahohi da ka'idojin gudanar da aiki domin karawa mazaunan kwarewar gudanar da aiki. Ya zuwa karshen shekarar 2019, akwai cibiyoyin samar da ayyukan yi 104 a matakin yankuna ko matakin dake gaba da shi, da kuma kananan cibiyoyin samar da tabbacin aikin yi 8,668. Wadannan sun samar da hidimomin samar da ayyuka sama da miliyan 20 ga mazauna yankin. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China