Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Xinjiang ba ta taba hana al'ummarta ciki har da 'yan kabilar Uygur zirga-zirga ba
2020-06-20 20:45:36        cri
Mataimakin shugaban hukumar tsaron al'umma ta jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, Yalqun Yaqup, ya bayyana cewa, a cikin shirin dokar kare hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2020 da Amurka ta zartas da shi, an ce wai Xinjiang ta tsara manufofin nuna bambanci ga 'yan kananan kabilu, ciki har da kwace musu wasu hakkokin al'umma da na siyasa da suka hada da zirga-zirga, da sadarwa, da samun shari'a mai adalci. A cewar Yalqun Yaqup, duk wannan furuci ya jirkita gaskiya kuma bata sunan kasar Sin ake yi.

A halin yanzu akwai dubun-dubatar 'yan asalin jihar Xinjiang wadanda ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a kasashe daban-daban, kuma al'ummomi a jihar suna iya mu'amala da 'yan uwansu dake kasashen waje cikin 'yanci kuma ba tare da wata matsala ba. A Xinjiang, idan wani mutum bai aikata mummunan laifi da za a hana shi fita waje ba, to zai iya tafiya kasashen waje cikin 'yanci.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China