![]() |
|
2020-07-18 20:48:16 cri |
A watan Satumban shekarar 2018, hukumomi masu ruwa da tsaki suka bayyana ginin hanyoyin shiga masallacin Jiami dake yankin Yecheng na jihar Xinjiang a matsayin masu hadari a mataki na D. Domin kare lafiyar masu ibada da tabbatar da gudanar harkokin ibada ba tare da matsala ba, aka gyara gine-ginen bisa amincewar hukumar kula da harkokin addinai ta gwamnatin Yecheng, a cikin watan Fabrerun shekarar 2019. Kuma tun daga ranar 6 ga watan Maris, aka fara amfani da wannan masallaci da aka yi wa kwaskwarima.
Yayin ake fama da cutar COVID 19, an dakatar da harkokin ibada tare da rufe masallatai a wasu kasashe a watan Ramadanan bana. Sai dai, an samu damar dakile yaduwar cutar cikin kankanin lokaci a jihar Xinjiang, don haka, aka bude wuraren ibada, ciki har da masallatai, inda aka ci gaba da harkoki kamar ko da yaushe a cikin watan na Ramadhan.(Mustapha Fa'iza)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China