Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a rage matakan gaggawa na tunkarar COVID-19 a Beijing
2020-07-20 11:04:14        cri
Gwamnatin birnin Beijing, ta sanar da cewa, daga yau Litinin, za a rage matakan gagagwa na tunkarar cutar COVID-19 daga mataki na II zuwa na III, a birnin.

A cewar Chen Bei, mataimakin sakatare janar na gwamnatin birnin, an yi nasarar dakile yaduwar cutar, bayan daukan managartan matakan dakile hanyoyin yaduwarta, tare kuma da inganta matakan kandagarki.

Ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar ba cikin kwanaki 14 a jere. Ya ce daga ranar 11 zuwa 19 ga watan Yuli, an samu matane 335 dake da nasaba da kasuwar ta Xinfadi, da aka tabbatar sun kamu da cutar a birnin.

Da yake bayani game da rage matakan, Chen Bei ya ce, yanzu jama'ar Beijing ba sa cikin hadari sosai na kamuwa da cutar, domin an dakile yaduwarta a unguwanni, haka zalika hadarin yada cutar daga birnin zuwa wasu wurare, shi ma ya ragu sosai.

A cewar mataimakin daraktan sashen raya birnin da aiwatar da gyare-gyare, Li Sufang, zuwa ranar Alhamis da ta gabata, galibin wuraren kasuwanci da na aikin gine-gine da kamfanoni da manyan kantuna a Beijing, sun koma bakin aiki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China