Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara inganta aikin yaki da COVID-19 a jihar Lagos ta Nijeriya
2020-06-29 10:34:29        cri
Yayin da Nijeriya ke ci gaba da samun karuwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19, hukumomi a jihar Lagos, cibiyar hada-hadar tattalin arzikin kasar, kuma inda cutar ta fi kamari, sun fadada ayyukan tunkarar cutar ta hanyar samar da dakunan gwaji 7 masu zaman kansu domin kara karfin gwaji da kuma asibitoci 3 masu zaman kansu, da nufin jinyar masu cutar.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Nijeriya NCDC, ta ce jimillar adadin masu cutar a kasar mafi yawan al'umma a Afrika ta kai 24,077, inda a ranar Asabar aka tabbatar sabbin mutane 779 sun kamu.

A yanzu haka, adadin masu fama da cutar ya tsaya ne kan 14,115 inda mutane 8,625 suka warke.

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Akin Abayomi, ya ce jihar ta kuduri niyyar dakile annobar, ta yadda harkokin kasuwanci za su ci gaba da gudana, da kuma inganta dabarun kiyaye lafiyar mazauna yayin da ake fuskantar barazana daga annobar.

A cewarsa, jihar ta fara tantancewa da sahalewa asibitoci masu zaman kansu, domin su taimaka a yakin da ake da cutar, bisa la'akari da bukatar inganta ayyukan tunkarar cutar da karfin gwaji da jinyar masu ita, musammam duba da yadda take matakin kara bazuwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China