Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Najeriya ya gana da babban sakataren ma'aikatar harkokin kasashen wajen Najeriyar
2020-07-01 13:49:54        cri

A ranar 30 ga watan Yuni, jakadan kasar Sin a Najeriya Zhou Pingjian, ya gana da babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen Najeriya Mustapha Lawal Sulaiman.

Zhou ya bayyana farin ciki game da yadda Najeriya ta halarci taron kolin musamman na Sin da Afrika don yaki da annobar COVID-19 da aka kira a 'yan kwanakin baya, da ma gudummawar da Najeriya ta bayar wajen gudanar da taron cikin nasara. Sannan ya yi karin haske game da matsayar da kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin ya dauka na amincewa da dokar tabbatar da tsaron kasa na yankin musamman na Hong Kong da kuma matsayar gwamnatin tsakiyar kasar Sin kan batun.

A nasa bangaren, Sulaiman ya bayyana aniyar karfafa tattaunawa da yin aiki tare da bangaren kasar Sin game da batutuwan dake shafar huldar kasashen biyu. Ya ce, Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, kuma batun da ya shafi dokar tsaron yankin Hong Kong batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin. Najeriya tana cikakken goyon baya da mutunta wannan batu, kuma ba za ta taba yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar ba. Ya ce sun yi amanna cewa Hong Kong zai ci gaba da samun kyakkyawar makomar da zaman lafiya a karkashin manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu".(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China