Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe gomman yan bindiga a haren da suka kaddamar ta jiragen sama a arewa maso yammacin kasar
2020-07-13 10:52:45        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa hare-haren da suka kaddamar ta jiragen sama ya yi sanadiyyar kashe 'yan bindiga masu yawa a maboyarsu dake daji a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

John Enenche, kakakin rundunar sojojin Najeriya ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jiragen saman yaki da jirage masu saukar ungulu dauke da manyan bindigogi da aka tura yankunan sun kaddamar da hare-haren a ranar 10 ga watan Yuli a dajin Kwiambana dake jahar Zamfara, a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

A cewar Enenche, wasu 'yan bindiga masu yawa wadanda hukumomin sojoji sun yi amanna barayin shanu ne an jikkata su a lokacin hare-haren da sojojin suka kaddamar ta jiragen sama.

Maharan sun yi kokarin tserewa da kafa da kuma kan babura kimanin 15.

A sanarwar da jami'in sojojin ya fitar ya ce, hare-haren sojojin ta sama ya biyo bayan samun bayanan sirri dake nuna cewa 'yan bindigar suna kokarin kafa sansaninsu, kuma ana zargin suna da alaka da kungiyar masu fafutukar jihadi a yammacin Afrika, karkashin jagorancin wani kasurgumin dan bindiga da ake kira Dodo Gede.

Kakakin sojojin ya ce, aikin samamen yana daya daga cikin muhimman ayyukan sintiri na hadin gwiwa da sojojin Najeriya suka kaddamar a shiyyar arewa maso yammacin kasar yankin da ya shafe shekaru yana fuskantar hare-hare. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China