Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da 'yan fashin tekun da suka farwa jirgin ruwan kasar Sin
2020-07-14 09:35:13        cri
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da wasu mutane 10 a gaban babbabr kotun jihar Lagos, bisa zarginsu da fashin jirgin ruwan kasar Sin.

Gwamnatin ta gurfanar da su ne bisa zargin aikata laifuffuka 3 da suka shafi fashin teku.

Mai gabatar da kara Magaji Labaran, ya zargi mutanen da aikata laifin ne a watan Mayu, a yankin ruwan kasa da kasa na Abidjan na kasar Cote D'Ivoire, dauke da muggan makamai.

Ana kuma zarginsu da laifin jefa ayarin jirgin mai suna FV Hai Lu Feng II, mallakin kamfanin kamun kifi na Haina, cikin tashin hankali, a kokarinsu na kwace iko da shi.

Magaji Labaran ya kara da cewa, lafuffukan sun keta tanadin sassa na 3 da 10 da kuma 12, na dokar fashin teku da sauran laifffukan da suka shafi sufurin ruwa ta 2019.

Sai dai, dukkan wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifukan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China