Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiin MDD ya bukaci a tunkarin batun sauyin yanayi don kawar da barazanar karancin abinci
2019-08-09 11:09:00        cri

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, yace rahoton baya bayan nan na majalisar gwamnatoci game da sauyin yanayi (IPCC) na cewa, wasu karin hujjoji ne dake tabbatar da cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa na shawo kan matsalar sauyin yanayin dake tunkarar duniya.

A cewar rahoton, matsalar sauyin yanayi ta kasance a matsayin wata babbar barazana dake tunkarar fannin samar da abinci a duniya baki daya, yayin da shirin inganta muhalli zai yi matukar taimakawa wajen kawar da dumamar yanayin duniya, da rage yawan sinadarai da ake fitarwa masu gurbata muhalli daga dukkan fannoni, kana zai taimaka wajen rage dumamar yanayin duniya da kasa da maki 2.

Stephane Dujarric, kakakin mista Guterres, yace, wadanda alkaluman bayanai da aka samu suna da muhimmanci ga taruka cimma matsaya na kimiyya wadanda ke tafe a nan gaba, kamar taron kolin sauyin yanayi na kasa da kasa da za'a gudanar a ranar 23 ga watan Satumba a matsayin wani muhimmin bangare na babban taron MDD karo na 74. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China