Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram 17 a jihar Borno
2020-07-09 09:44:13        cri
A kalla mayakan Boko Haram 17 ne sojojin Najeriya suka hallaka, yayin wata musayar wuta da sassan biyu suka gwabza a kan hanyar Damboa zuwa birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriyar John Enenche ya fitar a jiya, ya ce sassan biyu sun yi dauki ba dadin ne, bayan da mayakan Boko Haram suka yiwa sojojin kwantan bauna, lamarin da ya haifar da rasuwar wasu sojoji 2, kana wasu 4 suka jikkata.

John Enenche ya ce sojojin sun ci lagon mayakan 'yan ta'addan, wanda hakan ya sa ala tilas suka ranta a na kare. Tuni kuma aka kara yawan sojoji a yankin da lamarin ya auku, a wani mataki na tabbatar da cewa mayakan da suka tsere, ba su samu mafaka ba, yayin sabbin hare-hare da sojojin ke shirin kaddamarwa a wuraren da suke buya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China