Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an kasashen Afirka da dama sun yi maraba da matakin kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong
2020-07-13 15:08:04        cri


A yayin taro na 20 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 ne, aka zartas da dokar kare tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong na jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Dokar, ta yi cikakken bayani kan yadda za a hukunta wadanda suka aikata laifuffukan kokarin raba kasa, da juyin mulki, da ayyukan ta'addanci da zama 'yan kanzagin wasu bangarorin kasashen waje domin bata yanayin tsaron kasar Sin. Dokar tana da muhimmanci wajen hana wadanda suke son aikata wadannan laifuffuka guda hudu, da kiyaye manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu", da kare tsaron kasa da kuma tabbatar da ci gaban yankin Hong Kong.

Kwanan baya, manyan jami'an kasashen Afirka da dama sun nuna amincewa da maraba da matakin kafa wannan doka domin kare tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, inda suka zargi wasu kasashen dake neman tsoma baki a harkokin cikin gidan Sin.

Shugaban kungiyar matasa ta jam'iyyar kawance ta Mali, kana shugaban majalisar dokokin kasar Mali, Moussa Timbine ya bayyana cewa, harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kare tsaro da zaman lafiya a yankin Hong Kong babban nauyi ne dake wuyan gwamnatin kasar Sin. A don haka muna maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong, kuma muna goyon bayan gwamnatin kasar Sin wajen kiyaye ikon mulkin kanta da tsaron kanta. Bai kamata kasashen ketare su tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin ba, balle ma, bata yanayin tsaron kasar Sin ta hanyar yin amfani da batun yankin Hong Kong, ko kuma bata manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu".

Haka kuma, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Masar Salah Adly ya nuna cewa, kasar Sin tana da ikon kafa dokoki da daukar matakai domin kare tsaron kasarta, da adawa da wadanda suke neman bata sunan kasar Sin, ko tsoma baki a harkokin cikin gidanta.

A nata bangare, jam'iyya mai mulki ta ANC ta kasar Afirka ta Kudu ta fidda wata sanarwa, inda ta ce, bisa ka'idar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na birnin Bejing, tana son sake jaddada goyon bayanta ga matsayin kasar Sin kan batun yankin Hong Kong, da goyon bayan kokarin da kasar Sin take yi na kare tsaron kasa a yankin Hong Kong.

Ministan harkokin wajen kasar Guinea Mamadi Toure ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai 'yanci, kuma yankin Hong Kong wani bangare na kasar Sin, kana harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne, don haka, bai dace wasu kasashe su tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong ba. Ita ma kasar Guinea tana mutunta dadadden zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana goyon bayan kasar Sin game da matsayinta kan batutuwan dake shafar yankin Hong Kong.

Ita ma, ministar harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu, Beatrice Khamisa Wani-Noah ta bayyana cewa, yankin Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, saboda haka, ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba, kuma harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Gwamnatin kasar tana goyon bayan kasar Sin kan manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu", kuma, kasar Sin tana kiyaye tsaron kasarta bisa dokoki yadda ya kamata, da ci gaba da samun zaman lafiya a yankin Hong Kong ya dace da moriyar bangarori daban daban da abin ya shafa. Ya kamata kasashen da abin ya shafa su martaba kundin tsarin MDD, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da harkokin yankin Hong Kong.

Haka kuma, shugaban jam'iyya mai mulkin kasar Mauritania, Sidi Mohamed Ould Taleb Amar ya bayyana cewa, muna girmama ikon mulkin kan kasar Sin da cikakkun yankunan kasar, muna kuma maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong. Kasar Sin ta kafa wannan doka a lokacin da ya dace, kuma hakan zai ba da tabbaci wajen aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" yadda ya kamata a yankin Hong Kong.

Ban da haka kuma, ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fidda sanarwar cewa, gwamnatin kasar tana goyon bayan kasar Sin wajen kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, domin tabbatar da ci gaban yankin Hong Kong da kuma kare 'yanci da tsaron kasa.

A nasa bangare kuma, shugaban kungiyar zumunta tsakanin Sin da Burkina Faso ta majalisar dokokin kasar Burkina Faso, Bienvenue Bakyono ya bayyana cewa, kungiyar na tsayawa tsayin daka wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Burkina Faso. A matsayin gada tsakanin hukumomin kafa dokoki da mu'amalar al'umma a tsakanin kasashen biyu, kungiyar tana goyon bayan matakan kasashen biyu ta fuskar karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban. Dangane da batun dake shafar yankin Hong Kong kuma, tana maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong, ta kuma yaba wa kasar Sin game da kokarinta na kare 'yancin da raya yankin Hong Kong. Kuma, kungiyar za ta yi cikakken bayani ga mambobin kungiyar da majalisar dokokin kasa, domin kara ilimantar da su, ta yadda za su kara nuna goyon baya ga kasar Sin.

Idan muka kalli sauran kasashen duniya, za a fahimci cewa, kafa dokar tsaron kasa, iko ne dake hannun gwamnatin ko wace kasa, kuma, babu wata kasa da za ta yi hakuri kan wadanda suke neman bata yanayin tsaronta. Kasar Sin ta kafa dokar tsaron kasa bisa ka'idoji da dokokin kasa da kasa, kana, gwamnatin kasar tana tafiyar da kasa bisa manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" da bukatun yankin Hong Kong, kuma wannan manufa ba ta taba haddasa illa ga 'yancin yankin Hong Kong ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China