Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labarin Li Ji mai kishin kasa a Hong Kong
2020-07-05 17:26:20        cri

Tun da aka samu tashin-tashina a yankin musamman na Hong Kong, akwai mazauna yankin da dama wadanda suka nuna goyon-bayansu ga 'yan sanda, da rashin amincewa ga tada rikici, tare kuma da fatan ganin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Har ma mazauna Hong Kong da yawa sun kawar da shingayen da masu tada zaune-tsaye suka kafa a tituna, domin nuna takaici gami da rashin goyon-bayansu duk da cewa suna fuskantar hadari. Wadannan mutanen Hong Kong suna son nunawa duniya bukatarsu na dakatar da ayyukan tada rigima, da farfado da zaman doka da oda tun da wuri. Li Ji na daya daga cikinsu.

Li, mai yara uku, wani malami ne dake koyarwa a wata makarantar firamare dake yankin Hong Kong. Kuma irin abun da ya yi a shekara ta 2019, ya nunawa dukkan yara yadda yake kishin kasarsa wato kasar Sin.

A yayin da yake fuskantar rikicin da masu sanye da bakaken tufafi suke kokarin tayarwa a wata babbar kasuwa a Hong Kong, Li Ji wanda ke rike da yaransa uku, ya rera taken kasar Sin sau da dama da babbar murya. Ko da yake ya ji rauni, amma bai tsaya rera taken kasa ba. Li ya ce, makamin da yake dashi kadai, shine rera taken kasa da babbar murya, domin nunawa masu tada zaune-tsayen cewa, abun da suka aikata babban laifi ne, kuma a matsayinsu na 'yan kasar Sin, ya kamata su nuna kishin kasa maimaikon su tada rikici.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China