Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani ba'amurke wanda ke kokarin bayyanawa duniya gaskiyar abun dake wakana a Hong Kong
2020-07-05 17:33:57        cri

Duk duniya ta maida hankali kan abubuwan da suke wakana a yankin Hong Kong, amma sanin ainihin abubuwan da suka faru ba abu ne mai sauki ba. Wasu kafafen yada labaran kasashen yamma ba su ruwaito rahotanni na gaskiya da inganci kan rikicin da ya faru a Hong Kong ba, da zummar shafawa kasar Sin kashin kaji gami da yunkurin kawo tsaiko ga ci gaban kasar. Amma duk da haka, akwai wasu baki 'yan kasashen waje da suka san Hong Kong sosai, wadanda suke kokarin shaidawa duniya abubuwan da suka ji suka gani a yankin. Nathan Rich na daya daga cikinsu, wato wani kwararren mai sana'ar shirya fina-finai ne dan asaslin kasar Amurka.

Tun daga shekara ta 2018, Nathan Rich, ya fara tsara bidiyo ta kafar intanet dangane da abubuwan da suka shafi kasar Sin, a wani kokari na kawar da rade-radi gami da rashin fahimta kan kasar Sin. Tun bayan da aka samu tashin-tashina a yankin Hong Kong, ya zuwa yanzu, Nathan Rich yana himmatuwa wajen fadakar da al'umma kan ainihin abubuwan da suka faru cikin bidiyon da ya tsara ta intanet, wadanda ke jawo hankali sosai da sosai.

Nathan Rich ya ce, yana fatan bidiyon da ya tsara za su taimakawa masu tada rikici kara fahimtar kasar Sin, da bada gudummawarsa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin musamman na Hong Kong.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China