Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Afrika: Dokar Tsaron Kasa A Hong Kong Za Ta Tabbatar Da Wadatar Yankin
2020-07-09 14:00:51        cri


Aminu Bashir Wali, tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya, ya taba zama jakadan Nijeriya a kasar Sin. A yayin da ya yi aiki a kasar Sin, ya taba kai ziyara yankunan Hong Kong da Macao, inda ya kara saninsa kan yadda kasar Sin take aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulkin biyu" yadda ya kamata a yankunan.

Yayin da yake zantawa da wakilinmu a kwanan baya, malam Wali ya nuna cewa, dokar tsaron kasa a Hong Kong, tana taimakawa wajen tabbatar da wadata da kwanciyar hankali a yankin, wanda ke matsayin cibiyar kasa da kasa ta fuskar hada-hadar kudi da ciniki.

Dangane da aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong, Wali ya nuna cewa, Hong Kong, wani yanki ne na kasar Sin. Kuma kasar Sin na da ikon tsara dokoki masu nasaba da yankin, don hana ayyukan gurgunta tsaron kasa a yankin.

An samu barkewar tarzoma a Hong Kong a shekarar 2019 saboda mahukuntan yankin sun gabatar da shawarar yin garambawul kan batutuwan da suka shafi masu aikata laifi da suke guduwa. Masu yunkurin samun 'yanci kan Hong Kong, da 'yan a-ware masu tsattsauran ra'ayi sun fara tada zaune tsaye, suna kawo illa ga yadda kasar Sin take aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a Hong Kong.

A ganin Wali, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ba za ta kawar da kai daga abubuwan da suke faruwa a Hong Kong ba. Kamar yadda dukkan gwamnatocin kasashe wadanda suke sauke nauyin dake wuyansu suke yi, gwamnatin tsakiyar kasar Sin na sauke nauyin tabbatar da tsaron kai a yankin na Hong Kong. A cewar Wali, "Ina mara wa gwamnatin tsakiyar kasar Sin baya sosai, game da matakan da take dauka a yankin Hong Kong. A cikin dogon lokaci, duk da yawan suka da wasu suka yi kan kudurin kasar Sin, dawo da zaman lafiya da tsari, da oda a yankin Hong Kong, zai dace da muradun gamayyar kasashen duniya."

Kwanan baya, kasashe kusan 80, ciki had da kasa ta Nijeriya, sun yi jawabi a taron kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD, inda suka nuna goyon baya, kan yadda kasar Sin ta tsara dokar tabbatar da tsaron kasa a Hong Kong, sun kuma nuna cewa, kamata ya yi kasashen duniya su mutunta manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, su ki amincewa da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata kasa bisa hujjar kiyaye hakkin dan Adam.

A ganin Wali, an tsara dokar tsaron kasa a Hong Kong ne, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da kuma kiyaye mafi yawancin al'ummar Hong Kong daga tashin hankali a wurin, a maimakon saka musu wani tarnaki. Kuma wasu kasashen yammacin duniya sun sossoki dokar ne kawai domin matsa wa kasar Sin lamba. Wali ya ba da misali da cewa, "Idan an ta da rikici irin na Hong Kong a yankin Northern Ireland ko Scotland na kasar Birtaniya, to kuwa tabbas gwamnatin Birtaniya za ta dauki matakai, ba za ta kawar da kai ba. Saboda haka, ya zama tilas gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta dauki matakai, don kwantar da kura a yankin na Hong Kong. Wadanda suke zargin Sin, ba su fahimci hakikanin abubuwan dake faruwa ba. Ta kafar telibijin, mutane daga sassa daban daban na duniya sun kara fahimtar su, game da abubuwan da suka faru a Hong Kong a bara. Ma iya cewa, yankin na Hong Kong, yana cikin yanayi na zaman ta ci barkatai a bara."

Aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong, ya kuma jawo hankalin shahararren masanin kasar Namibiya Jairos Kangira. Yayin da yake zantawa da wakilinmu, ya nuna cewa, dokar za ta kare Hong Kong mai tsaro da kwanciyar hankali daga tsoma baki da wasu suke neman yi.

A ganin Kangira, daukacin al'ummar kasar Sin ciki had da al'ummar Hong Kong, sun zabi aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", haka kuma lamarin yake game da dokar tsaron kasa a Hong Kong. Yayin da ake murnar cika shekaru 23 da komawar Hong Kong hannun gwamnatin kasar Sin, yadda ake aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin, na yi wa wasu gargadi da cewa, kada su tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin. Ya kuma shaida aniyar gwamnatin tsakiyar kasar Sin, ta kiyaye wadata da kwanciyar hankali a Hong Kong.

Masanin ya kara da cewa, ko wace kasa a duniya na mayar da tsaron kanta a gaban komai, ta yadda ba za a lahanta tsaron kasa ba. A cewar masanin, "A Namibiya da sauran kasashen duniya, tsaron kasa na da matukar muhimmanci. Ya kamata a mutunta kokarin da kasar Sin take yi wajen kiyaye tsaron kanta. Kasar Sin ba ta bukatar amincewar sauran kasashe kan tsara dokokinta a gida. Kasar Sin na da ikonta na yin zabi da kanta." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China