Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakiliyar matasan yankin Hong Kong na goyon bayan kafa dokar kiyaye tsaron kasa a yankin
2020-07-11 17:34:53        cri
Jiya Juma'a bisa agogon Switzerland, mambar kungiyar dake rajin yayata manufofin MDD a kasar Sin, kuma mambar kwamitin raya harkokin matasan yankin musamman na Hong Kong, Lin Lin, ta gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin taron kungiyar kare hakkin bil Adama ta MDD, inda ta yi tir da rikice-rikicen da suka faru a yankin Hong Kong da kuma tsoma bakin da wasu kasashen ketare suke yi a kan harkokin yankin, kana ta nuna goyon baya ga kafa dokar kiyaye tsaron kasa a yankin.

Lin Lin ta bayyana a cikin jawabinta cewa, an kwace Hong Kong da karfin makamai daga hannun kasar Sin, inda ta kasance karkashin mulkin mallaka, kuma a shekarar 1997 aka maido da yankin karkashin mulkin kasar Sin, tana mai cewa, wannan abun farin ciki ne.

A cewarta, 2019, shekara ce ta bakin ciki a yankin Hong Kong, ganin cewa a wannan shekara yankin ya kasance wani wuri na tashin hankali. Ta ce kafofin watsa labaru da 'yan siyasar wasu kasashen ketare sun yi nufin halatta ayyukan nuna karfin tuwo da aka yi a yankin, kuma sun yi ta tsorata wadanda suke da bambancin ra'ayi da su.

Lin Lin ta kara bayyana cewa, jama'ar yankin Hong Kong ba za su yi hakuri da rikici ba. A watan Yunin bana, mazauna yankin miliyan 2.9 suka sanya hannu don nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin wajen tsara dokar kiyaye tsaron kasa a yankin. A cewarta, akwai bukatar su sake gina birninsu. Ba za su yarda a kara aikata rikici a Hong Kong ba, ta ce an riga an yi watsi da mulkin mallaka, don haka sai masu adawa da kasar Sin su nisanci yankin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China