Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na gaggauta farfado da tattalin arziki
2020-06-18 11:50:35        cri

Sakamakon komawa bakin aiki, da farfado da ayyuka a sassa daban daban na kasar Sin, ya sa an maido da zaman rayuwar jama'a a kasar sannu a hankali. Wasu alkaluman da aka gabatar a kwanan baya, sun shaida cewa, kasar Sin tana gaggauta farfado da tattalin arzikinta.

A ranar 11 ga wata, yawan wutar lantarki da aka yi amfani da ita a duk fadin kasar Sin, ta kai matsayin koli a bana, wanda ya fi na lokacin hunturu kafin barkewar annobar COVID-19 yawa. Ban da haka kuma, wasu alkaluman da suka shafi yin jigilar kaya a kasar Sin sun karu, da kashi 0.8 cikin kashi dari a watan Mayun bana, a maimakon raguwar kashi 1.2 cikin kashi dari a watan Afrilun bana.

Sakamakon gaggauta farfado da tattalin arzikin kasar Sin, ya sa karin kamfanoni su karfafa aniyar zuba jari a kasar. A lardin Anhui, kamfanin Volkswagen Group na kasar Jamus, ya kara zuba jarin kudin Euro biliyan 2, wajen bunkasa motoci masu amfani da wutar lantarki.

A birnin Tianjin kuwa, kamfanin Nestle ya kara zuba jari na kudin Sin RMB yuan miliyan 730, wajen sayen sabbin nau'o'in samar da abinci. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China