Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu kamuwa da COVID-19 na kara yawa a jihohin Amurka, yayin da ake ci gaba da kokarin farfado da harkoki
2020-06-22 10:41:08        cri

Jihohin Amurka da dama sun samu karuwar yawan masu cutar COVID-19, yayin da ake ci gaba da komawa aiki a fadin kasar, lamarin da ka iya tarnaki ga farfadowar harkokin.

Misali, alkaluma daga hukumar lafiya ta jihar Florida dake kudu maso gabashin kasar, sun nuna cewa, an samu sabbin mutane 4,049 da suka kamu da cutar a ranar Asabar, adadin mafi yawa da aka yi ta samu cikin kwanaki 3 a jere.

Bisa rahoton jaridar New York Times, an samu adadi mafi yawa na sabbin wadanda suka kamu da cutar a kudancin Carolina da Missouri da Nevada da Arizona da Utah da Montana a ranar Asabar, inda ya ce California da Texas da Alabama da Oklahoma da Oregon, sun riga sun kai wannan matsayi tun a farkon makon da ya gabata.

A cewar alkaluma daga jami'ar John Hopkins, zuwa jiya da rana, sama da mutane miliyan 2.2 aka tabbatar sun kamu da cutar a Amurka, inda mutane sama da 119,800 suka mutu.

Sama da mutane 30,000 ne suka kamu da cutar daga ranar Juma'a zuwa Asabar a fadin kasar, lamarin da ya nuna karuwar adadin masu cutar a kasar, duk da raguwar adadin da aka samu a jihohin kasar sama da 10, ciki har da jihohin New York da New Jersey. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China