![]() |
|
2019-09-17 09:37:26 cri |
Bugu da kari, kasashen biyu sun amince su zurfafa hadin kansu a fannin yaki da ta'addanci, ta hanyar musayar muhimman bayanai da kwarewa. Kamar yadda ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka bayyana cikin wata sanarwa bayan ganawarsu.
Da suke karin haske, ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita da takwaransa na Senegal Amadou Ba, sun yaba da dadaddiyar alaka mai inganci dake tsakanin kasashen biyu, da ci gaban da aka samu karkashin hadin gwiwa, musamman a fannonin kiwon lafiya da aikin gona, da sufuri, da kiwon kifi, da kuma diflomasiya. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China