Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya gabatar da taron gangamin yakin neman zabe a karo na farko tun bayan barkewar COVID-19
2020-06-21 17:28:43        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, wanda jam'iyyarsa ta Republican ta baiwa takarar neman yin ta zarce a tsakiyar watan Maris na bana ya shirya taron gangamin yakin neman zaben shugabancin kasar Amurka a karon farko a jiya 20 ga wata tun bayan barkewar annobar COVID-19.

Dubban mutane sun taru a birnin Tulsa na jihar Oklahoma, amma kafin taron, tawagar shirya takarar Trump ta tabbatar cewa, an tabbatar da mambobi shida dake cikin tawagar sun kamu da cutar, kana fadar White House ta taba bayyana cewa, za a samar da kayan rufe baki da hanci ga wadanda za su halarci taron, amma ba dole ba ne su sanya takunkumin rufe fuskar, sai dai bidiyon da aka watsa kai tsaye ta talibijin ya nuna cewa, kusan daukacin 'yan kallo a wurin taron wadanda suka zauna a bayan Trump ba su rufe baki da hancinsu ba.

A cikin 'yan makwannin da suka gabata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihohi 20 na kasar, ciki har da jihar Oklahoma yana ta karuwa, alkaluman da jami'ar Johns Hopkins ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa yammacin jiya ranar 20 ga wata, agogon gabashin Amurka, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya kai sama da miliyan 2 da dubu 250, kana wadanda suka rasu sanadin cutar sun kai kusan dubu 120. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China