Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai sabani tsakanin Mike Pompeo da Donald Trump
2020-06-20 16:39:44        cri

Rahotanni sun ce, a cikin sabon littafin da tsohon mai taimakawa shugaban kasar Amurka ta fuskar tsaron kasa wato John Robert Bolton ya rubuta, an nuna wasu ayyukan da Donald Trump ya yi a wa'adin aikinsa na shugaban kasar, ciki har da hada muradun siyasar da yake kokarin cimmawa da manufofin dokokin shari'a da diflomasiyyar kasar. Bolton ya kuma ce, watakila ana ganin cewa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo na daya daga cikin magoya-bayan Trump, amma hakikanin gaskiya shi ne, yana kokarin bata sunan Trump a boye, kuma yana kalubalantar kokarin da Trump ya yi kan batun da ya shafi kasar Koriya ta Arewa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito rahotannin jaridar New York Times yana mai cewa, a yayin ganawar farko da Trump ya yi da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un a kasar Singapore, Pompeo ya mikawa Bolton wata takardar dake cewa, gaskiya Trump bai iya aiki ba ko kadan.

Amma shafin intanet na jaridar Wall Street Journal ya ce, Trump ya musunta abun da Bolton ya rubuta a sabon littafinsa, inda a cewarsa, Bolton makaryaci ne da kowa ya tsana a fadar White House.

Har wa yau, Trump ya nanata cewa, akwai alaka mai kyau a tsakaninsa da Pompeo, amma akasin haka, Bolton ya rubuta cewa, sau da dama Pompeo ya yi la'akari da yin murabus daga gwamnati.

Bugu da kari, rahotanni daga tashar intanet ta jaridar Los Angeles Times sun ce, majiyoyi sun nuna cewa, mai gabatar da kara yana tunanin ko zai tuhumi Bolton saboda ya tona asiri a sabon littafinsa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China