Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin kasar Namibia ya yaba wa dokar tsaron kasa da ta shafi Hong Kong
2020-07-04 21:21:28        cri
Wata jaridar kasar Namibia, ta wallafa sharhin Jairos Kangira, wani sanannen masani na kasar, mai taken " Manufar kasar Sin ta tabbatar da ikon cin gashin kai na Hong Kong" inda ya yabawa aikin zartar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong a kasar Sin.

A cewar masanin, yadda aka zartas da dokar zai zama wani muhimmin matakin da zai shiga tarihi. Ya ce bisa wannan matakin, kasar Sin tana sanar da wani sako ga bangarorin kasa da kasa, cewa, ba wanda zai iya tsoma baki a harkokinta na cikin gida, kana gwamnatin tsakiyar kasar na da cikakkiyar niyyar kare walwala da kwaciyar hankali a yankin Hong Kong.

Mista Kangira ya kara da cewa, tsaron kasa yana da matukar muhimmanci a idanun kasashe daban daban. Amma yankin Hong Kong ya sha fuskantar zanga-zangar nuna karfin tuwo, da tada zaune-tsaye da wasu matasan yankin suka yi da sunan "kare tsarin dimokuradiya", cikin watanni 12 da suka wuce. A cewar masanin, akwai yiwuwar samun wasu kasashen yammacin duniya dake goyon bayan rikicin da ake samu a Hong Kong, bisa la'akari da yanayin da ake ciki na gogayya, don samun ikon jagorantar tsarin tattalin arzikin duniya, musamman ma yadda kasar Sin take neman hadin gwiwa da kasashe daban daban don aiwatar da shawarar "Ziri Daya Da Hanya Daya". Ya kara da cewa, a wannan lokaci, zai yiwu wasu kasashen waje su nemi ta da rikici a Hong Kong, da zummar yi wa kasar Sin tarnaki, ta yadda ba za ta samu gogayya da su sosai ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China