Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu 'yan siyasar kasashen Afrika na goyon bayan dokar tsaron kasa ta Hong Kong
2020-06-08 13:48:47        cri
A baya-bayan nan, 'yan siyasa a wasu kasashen Afrika, sun bayyana ta hanyoyi da dama cewa, batutuwan da suka shafi Hong Kong, batutuwa ne na cikin gidan kasar Sin, kuma zartar da dokar tsaron kasa kan Hong Kong, muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka wajen karewa da inganta manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu", da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Hong Kong, da kare cikakken 'yanci da tsaron kasar Sin. Haka zalika, ta bada gudunmuwa ga tsaro da zaman lafiya a duniya.

A cewar mninistan yada labarai na Jamhuriyar Niger, Habi Mahamadou Salissou, matakin kasar Sin na zartar da dokar tsaron kasa kan HK, ya dace da kundin tsarin mulki da dokokin yankin musammam na HK, kuma yana bisa doron doka mai karfi. Ya ce ba kare ci gaba da kwanciyar hankali a yankin kadai dokar take yi ba, har ma da kare 'yanci da hakkokin al'ummar Hong Kong. Ya kara da cewa, wannan batu ne na cikin gidan kasar Sin, wanda bai kamata wasu kasashe su sa baki ba, yana mai cewa ba su da wannan 'yancin, kuma Niger na goyon bayan bangaren kasar Sin.

Shi ma shugaban majalisar dokokin Mali, Moussa Timbinet, ya ce harkokin HK harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin yankin, halaltaccen hakki ne a kan gwamnatin kasar Sin. Ya ce suna goyon bayan matakan da majalisar dokokin kasar Sin ta dauka na zartar da dokar tsaron kasa akan HK da kuma kokarin da gwamnatin ke yi na kare cikakken 'yanci da tsaron kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China