![]() |
|
2019-10-17 13:53:45 cri |
Ahmed Gusau Bala ya taba zama karamin jakadan Najeriya dake Hong Kong a tsakanin shekarun 2017 - 2018. A yayin da yake zantawa da wakilinmu ya ce, ana gudanar da tsarin "kasa daya, tsarin mulki guda biyu" yadda ya kamata a yankin Hong Kong. Game da zanga-zangar nuna karfin tuwo da ayyukan lalata kayayyaki da aka ta yi na tsawon 'yan watanni a yankin, Bala ya ce, nuna karfin tuwo ba zai taimaka wajen warware duk wata matsala ba, rahotannin da wasu kafofin watsa labaru suka bayar da kalaman 'yan siyasa na yammacin duniya son zuciya ne. Harkokin yankin Hong Kong harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, sauran kasashe ba su da ikon tsoma baki ciki. (Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China