Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararren Nijeriya: Ya kamata kasashen Afirka su hada kai wajen habaka shawarar "ziri daya da hanya daya"
2020-07-03 13:04:35        cri

A ranar 1 ga wata, shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake kasar Nijeriya Charles Onunaiju ya gabatar da sharhi mai taken "shawarar ziri daya da hanya daya da farfadowar kasashen Afirka bayan annobar cutar COVID-19" a jaridar Blueprint ta kasar Nijeriya. A ganinsa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta dace da ka'idojin yin mu'amala, da gudanar da ayyuka cikin hadin gwiwa da cimma moriyar juna, za kuma ta inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da kuma habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashe maso tasowa, da ma tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba, lamarin da zai samar wa kasa da kasa kayayyakin da al'ummomin suke bukata. Ya ce, ya kamata kasashen Afirka su yi amfani da wannan dama ta habaka shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda za su farfado da kasashensu bayan annobar COVID-19.

Sharhin ya ce, duk da annobar COVID-19, hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" tana bunkasa, ana kuma aiwatar da shirye-shiryen da aka kulla yadda ya kamata, tare da sanya hannu kan sabbin shirye-shirye da dama. A farkon watanni uku na bana, karfin cinikayyar kasashen dake hadin gwiwa da kasar Sin kan shawarar ya karu da 3.2%, kuma, adadin jarin da aka zuba kai tsaye ya karu da 11.7%, duk da annobar da ake fuskata.

Kana daga watan Janairu zuwa watan Mayu, yawan tafiye-tafiyen jiragen kasa dake jigilar kayayyaki tsakanin Sin da Turai ya karu da 28%, a sa'i daya kuma, kayayyakin da aka jigilarsu ya karu da 32%. Kuma, gaba daya, an yi jigilar tan 12,524 na kayayyakin yaki da cutar COVID-19, lamarin da ya taimaka wajen hada kan kasa da kasa wajen yaki da cutar COVID-19 da ceton rayuka. A don haka, ya dace kasashen Afirka su yi amfani da wannan dama mai kyau, wajen habaka hadin gwiwarsu da ragowar kasashen duniya, ta yadda za a samu dauwamammen ci gaba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China