Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gabatar da jawabi a wajen babban taron hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya"
2020-06-18 21:53:05        cri
Yau Alhamis, an yi nasarar gudanar da babban taro ta kafar bidiyo na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Xi Jinping ya ce, annobar ba-zata ta COVID-19 tana ci gaba da kawo babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron al'ummar daukacin duniya, da illata tattalin arzikin duniya, kuma akwai wasu kasashe, musamman kasashen dake tasowa, wadanda ke fuskantar babbar matsalar koma-bayan tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma. A nasu bangaren, jama'ar kasar Sin suna fatan bada tasu gudummawa ga aikin yaki da annobar da farfado da tattalin arzikin duniya.

Xi ya ci gaba da cewa, ko a fannin dakile annobar, ko kuma a fannin farfado da tattalin arziki, akwai bukatar a zama tsintsiya madaurinki daya, wato a tsaya ga ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin na nacewa ga bin hanyar neman ci gaba cikin lumana, da samun moriya tare da sauran kasashe. Kuma Sin na fatan kara raya shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda za ta taimaka ga karfafa hadin-gwiwa da tinkarar kalubale, da tabbatar da lafiyar al'umma, da farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'umma, gami da neman ci gaba mai dorewa. Kazalika, Xi ya ce, ta hanyar raya shawarar "ziri daya da hanya daya", za'a ci gaba da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

Taron mai taken "inganta hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin 'ziri daya da hanya daya', domin tinkarar annobar COVID-19 kafada da kafada", ya samu halartar manyan jami'an gwamnati daga kasashe 25, tare da babban darektan hukumar WHO da mataimakin sakatare-janar na MDD da sauransu. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China