Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin da kamfanonin Sin suka zuba a kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" ya wuce dalar Amurka biliyan 100
2019-09-30 13:07:25        cri
Cikin 'yan shekarun nan, harkokin zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" suna ci gaba da bunkasuwa.

A jiya Lahadi, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, jimillar yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya", ta zarce dala biliyan dari 1. Kana, jarin da wadannan kasashe suka zuba a kasar Sin ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 48.

Qian Keming ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai na murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya ce, a 'yan shekarun nan, adadin ciniki dake tsakanin Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" yana ci gaba da karuwa cikin yanayi mai kyau, kana adadin kayayyakin da Sin ta fitar zuwa wadannan kasashe ya kai 30.1%, bisa dukkan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen ketare.

Kana, bisa labarin da aka samu, an ce, ana gudanar da ayyukan gina manyan shirye-shirye, da yankunan masana'antu a kasashen kamar yadda ake fata. An kaddamar da gadar Zumunci ta Sin da Maldives, da hanyar jirgin kasa tsakanin Addis Ababa da Djibouti, da kuma tashar jiragen ruwa ta Gwadar cikin nasara.

Haka kuma, Sin ta gina yankunan hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a wadannan kasashe. Gaba daya, ta zuba jari na dalar Amurka biliyan 30 a kasashen, lamarin da ya samar da guraben aikin yi sama da dubu dari 3 a wuraren. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China