![]() |
|
2019-12-28 17:27:22 cri |
A watan Maris din bana, shugaba Xi ya yada zangonsa na farko a kasar Italiya, inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan takardar bayani ta inganta ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya". A watan Nuwambar bana kuma, yayin da yake ziyara kasar Girka, Xi da takwaransa na kasar sun cimma matsaya kan inganta hadin-gwiwar kasashensu a wannan fanni.
Har wa yau, a babban dandalin tattaunawa karo na biyu na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" da aka yi a watan Afrilun bana a Beijing, shugaba Xi ya gabatar da wani muhimmin jawabi ga mahalarta taron sama da dubu shida, inda ya ce, ya kamata a kara maida hankali a fannin raya ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", domin neman ci gabansu mai inganci kuma yadda ya kamata.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China