Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin ta mika kayayyakin yaki da cutar COVID-19 karo na biyu ga Guinea
2020-07-02 16:03:29        cri
An gudanar da bikin mika kayayyakin yaki da cutar COVID-19 karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Guinea a birnin Conakry dake kasar Guinea, inda shugaban kasar Alpha Condé ya nuna godiya ga shugaban kasar Sin Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin da jama'arta domin sun kara samar da gudummawa da goyon baya ga kasarsa ta Guinea.

Jakadan Sin dake kasar Guinea Huang Wei ya halarci bikin, inda ya yi bayani game da shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a gun taron kolin Sin da Afirka kan yaki da cutar COVID-19, kana ya bayyana cewa, cutar ta yadu a dukkan sassan duniya, cutar abokiyar gaba ce ga dukkan 'yan Adam. Kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, da nuna goyon baya ga ayyukan yaki da cutar COVID-19 a Afirka, da kuma sada zumunta da kara yin hadin gwiwa tsakaninta da Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China