Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kasashen Afirka suna shirin farfado da tattalin arzikinsu yayin da suke tinkarar cutar COVID-19
2020-07-01 14:56:49        cri
Kasashen Afirka da dama suna ci gaba da tinkarar cutar COVID-19, inda wasu suka fara shirya farfado da tattalin arzikinsu.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Afirka ta Kudu ya zarce dubu 150 a ranar 30 ga watan Yuni. An fi samun karuwar mutanen da suke kamuwa da cutar a jihar Gauteng ta kasar, inda gwamnatin ke la'akari da sake aiwatar da matakan killace jihar, wannan ya shaida cewa, mai yiwuwa za a sake dakatar da ayyukan ciniki a jihar.

Wasu kasashen Afirka sun riga sun gabatar da shirin farfado da tattalin arzikinsu. Kasar Nijeriya za ta ci gaba da sassauta matakan kulle sannu a hankali. Tun daga ranar 1 ga watan Yuli, za a soke takaita zirga-zirgar mutane tsakanin jihohi, amma za a ci gaba da hana fita daga karfe 10 na dare zuwa karfe 4 na safe a dukkan kasar, kana an bukaci jama'ar kasar su rika sanya abin rufe baki da hanci in za su fita waje. Gwamnatin kasar ta shirya bude kos na daliban da suka kusan gama karatun makarantun firamare da na midil, don komawa makarantu da shiryawa jarrabawar gama karatunsu. Hakazalika kuma, kasar Senegal ta sanar da soke matakan dokar-ta-baci da na hana fita, tun daga karfe 11 na daren ranar 30 ga watan Yuni, kana za ta gabatar da shirin farfado da tattalin arzikinta a nan gaba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China