Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Financial Times: Kasar Sin ta kara jaddada matsayinta na zama daya daga kasashen dake kan gaba wajen zuba jari a duniya
2020-06-30 11:33:32        cri

Jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya, ta ba da rahoto a jiya Litinin cewa, kasar Sin ta kara jaddada matsayinta na zama daya daga cikin kasashen da ake rububin zuba jari a cikinta a duniya, duk da matsalar cutar COVID-19. Inda ta bayyana kasar dake yankin Asiya, a matsayin wurin ba kasafai ake samun irinsa ba, a wannan lokaci mai muhimmanci ga bangaren zuba jari.

Rahotanni na cewa, a watanni na farko na wannan shekara 2020 da muke ciki, kudaden kasar sun karu a kasuwar hannayen jari ta duniya nesa ba kusa ba, kana bangaren zuba jarin kasar zai ci gaba da bunkasa duk da matsalar da COVID-19 da ake fama da ita.

Jaridar ta ce, ci gaban da aka samu, ya kara nuna matsayin kasuwar kasar Sin, na kasancewa wurin zuba jari mafi kyau a lokacin da bangaren zuba jari ke fuskantar wani muhimmin canji, daga kwararar masu zuba jari zuwa raguwar farashin kadarori a lokacin da aka sayar da su a watan Maris, da yadda kasuwar ke kokarin daidaito yayin da ake ci gaba da fama da matsalar COVID-19.

A cewar jaridar, ana kara samun takarar zuba jari a kasuwar makamashin kasar Sin tsakanin cibiyoyin kudi na duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China