Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da manyan shugabannin fitattun kamfanonin kasa da kasa, wadanda suka zo birnin Beijing domin halartar taron koli karo na bakwai, na kwamitin hadin-gwiwar shugabannin kamfanonin duniya yau Alhamis, inda ya jaddada cewa, kasarsa za ta yi tsayin daka, wajen zurfafa yin kwaskwarima a gida, da fadada bude kofa ga kasashen ketare, da ci gaba da kyautata muhallin gudanar da kasuwanci bisa doka.
Firaminista Li ya kuma yi maraba da kamfanonin kasa da kasa, da su ci gaba da habaka zuba jari a kasar Sin, da more damammakin ci gaban kasar.(Murtala Zhang)