Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta ce baki 'yan kasuwa na matukar son zuba jari a kasar
2019-05-22 11:09:52        cri
A kwanakin baya ne kasar Amurka ta ce kara sanyawa hajojin kasar Sin harajin da ta yi ya sa wasu kamfanoni sun kaura daga Sin zuwa sauran kasashe. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang ya bayyana cewa, gaskiyar magana ita ce, har yanzu baki 'yan kasuwa na matukar sha'awar zuba jari a Sin, ita kuma kasar Sin har kullum na maraba da kamfanonin kasahen ketare da su zo kasar su zuba jari.

A wajen taron manema labarai da aka yi, Lu Kang ya ce, abun da Amurka ta yi na keta ka'idojin kasuwancin duniya ya kawo cikas ga kasuwannin kasa da kasa, ciki har da Sin da Amurka kanta. Amma kamfanonin kasashen duniya suna da nasu zabi wajen zuba jari. Lu ya ci gaba da cewa, baya ga wasu sanannun kamfanonin kasashen waje wadanda suka kara zuba jari a kasar Sin, ciki har da ExxonMobil da Tesla da BASF da BMW, har ma rahoton harkokin kamfanonin kasar Japan a kasashen waje a shekara ta 2018 da hukumar bunkasa harkokin kasuwancin kasar ta bayar ya nuna cewa, kamfanonin Japan sun ci gaba da nuna sha'awa ga kasuwannin kasar Sin.

Har wa yau, a wajen babban dandalin tattauna hadin-gwiwar kasa da kasa ta fuskar shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu da aka yi a Beijing, mahalarta taron sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin-gwiwa da darajarsu ta zarce dala biliyan 64.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China