Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lu Kang: Har yanzu 'yan kasuwan kasashen waje na da tabbaci kan zuba jari a kasar Sin
2019-05-31 10:29:45        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, wani binciken yanayin kasuwanci na shekarar 2019 da kungiyar majalisar 'yan kasuwar Turai dake gudanar da harkokin kasuwanci a kasar Sin ta gudanar, ya nuna cewa, duk da harajin da kasar Amurka ta sanyawa kayayyakin kasar Sin, kamfanonin kasashen waje na rububin zuba jari a kasar Sin.

Lu Kang ya bayyana hakan ne, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa a taron manema labarai da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin game da binciken da kungiyar majalisar 'yan kasuwar Turai dake kasar Sin ta fitar.

Binciken ya nuna cewa, kaso 62 cikin 100 na wadanda aka zanta da su, suna daukar kasar Sin a matsayin daya daga cikin wurare uku na farko da a halin yanzu da ma nan gaba ke da makoma mai haske game da harkokin zuba jari, yayin da kaso 56 cikin 100 na wadanda aka zanta da su ke shirin kara zuba jari a kasar Sin.

Jami'in na kasar Sin ya ce, har kullum 'yan kasuwa na zabar kasashen da za su zuba jari da abokan hulda bisa la'akari da muradu da manufofinsu na kasuwa. Yana mai cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje.

Lu Kang ya ce, kasar Sin tana maraba da 'yan kasuwa na ketare da su zo su zuba jari a cikin kasar Sin, su kuma kaddamar da alakar cin moriyar juna. Kuma a shirye kasar Sin take wajen samar da daidaito na yanayin kasuwanci ga baki masu zuba jari da yin komai a bayyane, da samar da ingataccen yanayi na zuba jari mai dorewa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China