Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Ghana na shirin tinkarar kalubalen cutar COVID-19
2020-06-28 16:19:00        cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sanar da cewa tattalin arzikin kasar zai iya jure kalubalen annobar COVID-19, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da jam'iyyar NPP mai mulkin kasar ta ayyana shugaban a matsayin mutumin da zai tsaya mata takara a zaben da za'a gudanar na shugaban kasa a watan Disamba.

Ya ce duk da irin mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki tun bayan da ya karbi ragamar mulkin kasar a shekarar 2017, gwamnatinsa tana yin aiki tukuru domin cimma muhimman nasarori game da kyautata makomar tattalin arzikin kasar a shekaru sama da uku da suka gabata.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da jam'iyyar NPP ta lamince masa ya tsaya takarar neman shugabancin kasar a zaben da za'a gudanar a watan Disamba.

Ya ce ba su yi wani shiri game da wannan matsalar da ba'a taba tsammanin faruwarta ba, amma sun tsara tattalin arzikin kasar ta yadda zai iya jure tinkarar matsanancin hali, za su gina kasar bisa hadin gwiwa tare da dukkan mutanen kasar Ghana idan annobar ta zo karshe. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China