Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana kimiyya a Ghana sun kera na'urar gano masu dauke da COVID-19
2020-04-29 10:52:58        cri

Masu nazarin kimiyya daga jami'ar kiwon lafiya ta kasar Ghana sun samar da wata na'urar ta RDT, wadda ke iya gano masu dauke da kwayar cutar COVID-19 cikin hanzari a kasar.

Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar Ghana da cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Noguchi Memorial Institute ne suka bayar da taimakon aikin samar da na'urar a cikin mako guda.

Ministan yada labarai na kasar Kojo Oppong-Nkrumah ya bayyana cewa, gwamatin kasar tana fatan na'urar za ta taimakawa aikin ganowa da kuma gwajin masu dauke da cutar a kasar ta Ghana. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China