Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wandanda suka kamu da COVID-19 ya kai 8,297 a kasar Ghana
2020-06-03 10:00:16        cri
Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Ghana, ya karu zuwa 8,297, inda aka samu karin sabbin mutane 227 da aka tabbatar sun kamu da cutar a jiya Talata.

Alkaluman da hukumar kula da lafiya ta kasar ta fitar, sun ce wasu mutane biyu dake jinya sun mutu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar zuwa 38.

Baya ga haka, wasu 39 sun warke, inda jimilar wadanda suka warke a kasar ta yammacin Afrika ya kai 2,986.

Shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya ce kafofin shiga kasar za su ci gaba da kasancewa rufe, har sai abun da hali ya yi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China