Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummar kasar Sin ta bada gudunmuwar kayayyakin lafiya da abinci ga yakin da Ghana take da COVID-19
2020-06-19 11:22:07        cri
Al'ummar Sinawa da ofishin jakadancin kasar Sin a Ghana, sun bada gudunmuwar kayayyaki daban daban na lafiya da abinci ga Jam'iar nazarin likitanci ta Ghana, a wani yunkuri na taimakawa kasar a yakin da take da COVID-19.

Kayayyakin sun hada da na'urorin taimakon numfashi 15 da makarin hanci 60, da wani makarin irin na likitoci 20,000, da rigunan kariya 120, da tabarau 100, da sauran wasu kayyakin abinci.

Jakadan kasar Sin a kasar Wang Shiting, ya ce yayin da ake fuskantar COVID-19, Sin da Ghana, da ma Sin da Afrika, sun fuskanci kalubale mai tsanani, kuma suna kokarin taimakawa juna, da fafutuka tare kafada-da-kafada.

Ya ce akwai bukatar ci gaba da yaki da annobar tare, yana mai alkawarin a shirye Sin take ta ci gaba da taimakawa nahiyar Afrika, ta hanyar samar da kwararru da kayayyaki, da kuma saukakawa nahiyar hanyar sayen kayayyaki daga kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China