Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jirgin ruwa mai dauke da jirgi mai nutso cikin teku dauke da mutane ya fara tafiya
2020-06-26 13:17:23        cri

Bayan kammala aikin gyaran fuska ga babban jirgin ruwa mai dauke da jirgi mai nutso cikin teku dauke da mutane, wanda ke dauke da na'urorin binciken kimiyya kirar kasar Sin, mai samfurin "Tansuo lamba 2", ya fara tafiya da safiyar jiya Alhamis daga lardin Fujian.

A matsayin irin wannan babban jirgin ruwan na farko a kasar Sin, wanda ya iya daukar jirgi mai nutso cikin teku dauke da mutane, an kammala aikin gyare-gyare ga jirgin cikin watannin 18 kacal, kuma ya fara tafiya zuwa birnin Sanya.

Da farko dai, jirgin ya yi aikin injiniya, bayan an yi masa gyara kuma, yana da karfin nazari a cikin teku mai zurfi. Ban da wannan kuma, yana dauke da wasu na'urorin nazari a cikin teku, ciki hadda jirgi mai nutso dauke da mutane cikin teku mai zurfin fiye da mita dubu 10, wanda ya kasance jirgi mafi girma a duniya a wannan fanni.

Bayan an yi masa gyaran fuska, karfinsa ya karu kuma ya dace da aikin nazari a cikin teku mai zurfi, wato shimfidadden karfe ko bene na wannan jigri na iya daukar abu mai nauyi, dakunan nazari sun habaka matuka, kayayyakin da zai dauka sun karu sosai, kuma dakunan kwana sun samu ingantuwa da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China