Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta cimma nasarar harba tauraron Bil Adam na karshe na BeiDou na hidimar taswira
2020-06-23 11:14:28        cri

Yau Talata da misalin karfe 9 da mintoci 43 na safe, Sin ta cimma nasarar harba tauraron Bil Adam na Beidou mai lamba 55, wato tauraron Bil Adam na karshe na Beidou 3 na hidimar taswira. Hakan na nuna cewa, an cimma shirin kafa tsarin tauraron Bil Adam na hidimar taswira a duniya, mai amfani da tauraron Bil Adama na Beidou 3, kafin rabin shekara da aka tsara.

Bayan Sin ta cimma wannan gagarumar nasara, sashi mai kula da sararin sama na MDD, ya gabatar da sakon bidiyo, don taya murnar kafa wannan tsari, da kuma jinjinawa taimakon da tsarin Beidou ke bayarwa, wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kuma yabawa babbar gudunmawar da ya bayar, a fannin amfani da sararin sama lami lafiya, da shiga aikin MDD na nazarin sararin sama da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China