Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta harba taurarin dan-Adam guda biyu kamar yadda aka tsara
2020-06-01 11:45:01        cri

A jiya Lahadi da misalin karfe 4 da mintuna 53 na yamma bisa agogon Beijing na kasar Sin, kasar ta yi nasarar harba taurarin dan-Adam guda biyu zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar.

An dai harba taurarin dan-Adam din ne ta hanyar amfani da rokar Long March-2D. Daya daga cikin taurarin dan-Adam din, mai suna Gaofen-9, yana iya daukar ingantattun hotuna daga nisan kimanin mita guda.

Za kuma a yi amfani da shi wajen safiyon kasa, da tsara birane da aikin gina hanyoyi da kiyasin yabanyan irin shuka da kuma rage radadin bala'i. Baya ga ayyukan da zai gudanar a kasashen da suke cikin shawarar Ziri daya da hanya daya.

Kamfanin nazarin harkokin sararin samaniya na HEAD Aerospace Techonology Co Ltd dake Beijing ne, shi ne ya kera daya tauraron dan-Adam din mai suna HEAD-4. Zai kuma iya gudanar da aikin tattara bayanai a yayin da yake sararin samaniya, ciki har da kan jiragen ruwa da na sama da bayanan da suka shafi harkokin Intanet. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China