Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: An dage lokacin harba tauraron dan adam na karshe na BeiDou na hidimar taswira
2020-06-16 10:01:37        cri

An dage lokacin harba tauraron dan adam na karshe samfurin BeiDou mai aikin hidimar taswira na kasar Sin. Hakan dai ya biyo bayan wata matsala da aka gano rokar harba tauraron mai lamba March-3B na da ita.

An gano wannan matsala ce dai lokacin da ake aikin gwajin harba tauraron, kamar dai yadda ofishin kula da harba tauraron na kasa ya tabbatar.

Kafin hakan, an shirya harba wannan tauraro ne a Talatar nan, sai dai kuma a yanzu, an dage hakan zuwa wani lokaci da za a fitar a nan gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China